Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Bindiga sun kai hari a Wukari bayan kai hari a Kanon Najeriya

Wasu ‘Yan bindiga da ba a tantance ba sun kai hari a garin Wukari na Jahar Taraba tare da yin fashi a bankuna, wannan kuma na zuwa ne bayan wasu ‘Yan bindigar sun kai hari a yankin Dala da Fanshekara a birnin Kano inda suka yi musayar wuta da ‘Yan Sanda.

Wani hari da aka taba kai wa a garin Kano inda aka yi garkuwa da wani bajamushe
Wani hari da aka taba kai wa a garin Kano inda aka yi garkuwa da wani bajamushe REUTERS/Stringer
Talla

Rahotanni sun ce, ‘Yan Sandan Kano sun yi nasarar kwantar da harin, sai dai kuma an samu rasa rayukan mutane hudu kamar yadda mazauna Kano suka tabbatar.

Da daren Jiya Talata Wasu ‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a bankunan Wukari inda suka saci makudan kudade.

Rahotanni sun ce an kwashe daren jiya Barayin suna fashi a Wukari ba tare da jin duriyar Jami’an tsaron ba domin  kokarin hana 'Yan Bindigar.

Kodayake da safiyar Laraba, mazauna Wukari sun ce Jami’an tsaro sun karbe ikon Garin bayan ‘Yan fashin sun gudu.

Rahotanni a garin Kano sun ce an samu tashin jerin bama bamai Biyar a Ofishin ‘Yan Sanda a unguwar Goron Dutse.

Garin Kano dai ya yi fama da jerin hare hare wadanda kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin daukar Nauyi. A watan Janairu an kai wani hari wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 185.

Sai dai yawancin hare haren Kano ana kai su ne a ginin Ofishin Jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.