Isa ga babban shafi
Najeriya

Bama-bamai sun fashe a birnin Kano tare da kashe mutane fiye da 20

Rahotanni daga birnin Kano da ke arewacin Najeriya sun ce akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon fashewar bama-bamai a marecen yau.

Wani hari da aka kai wa birnin Kano ranar 22 ga watan disambar 2012
Wani hari da aka kai wa birnin Kano ranar 22 ga watan disambar 2012 REUTERS/Stringer
Talla

Shaidu sun ce an kai harun ne a kan wata motar da ke makare da fasinja, kuma motoci uku ne suka kone kurmus sakamakon wannan fashewa. Kuma lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jama’a suka yi cincirindo domi shiga mota a wata tashar mota da ke kusa da unguwar Sabon Gari.

Birnin na Kano wanda shi ne gari na biyu mafi girma a kasar, yana daya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro tun daga lokacin da kungiyar nan ta Boko Haram ta soma gudanar da ayyukanta a Najeriya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.