Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

‘Yan tawayen Seleka sun bukaci Bozize ya yi murabus

A wata sanarwa, Kakakin ‘Yan tawayen Seleka Kanal Sylvain Bordas na kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya mayar da martani ga shugaba Francois Bozize wanda ya bayar da umurnin sakin ‘Yan siyasar da aka cafke tare da dage dokar ta baci domin biya wa ‘Yan tawayen da bukatunsu.

Shugaban Afrika ta tsakiya François Bozizé da shugaban 'Yan tawayen Seleka Michel Djotodia, a lokacin da suke zaman sasantawa a birnin Libreville na Gabon.
Shugaban Afrika ta tsakiya François Bozizé da shugaban 'Yan tawayen Seleka Michel Djotodia, a lokacin da suke zaman sasantawa a birnin Libreville na Gabon. AFP PHOTO / STEVE JORDAN
Talla

Kakakin kungiyar ‘Yan tawayen ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran Reuters cewa abinda suke bukata shi ne shugaba Bozize ya yi murabus.

Bayan Sakin ‘Yan fursunan Siyasa da janye shingen bincike, ‘Yan tawayen sun bukaci ficewar dakarun Afrika ta kudu kimanin 400 daga kasar.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargaba game da rikicin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, lamarin da ke gurgunta tattalin arzikin kasar tun samun ‘yanci daga Faransa a 1960.

Kasar Jamhuriyyar Afrika ta kudu tana da arzikin albarkatun kasa da suka hada zinari da Uranium amma kuma kasar tana cikin jerin kasashen da ke fama da talauci saboda rikici kamar Chad da Sudan da Jamhuriyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.