Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

‘Yan tawayen Afrika ta tsakiya sun jajajirce sai Bozize ya yi murabus

An kasa cim ma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Afrika ta tsakiya da ‘Yan Tawaye a zaman sasanta juna da bangarorin biyu ke yi a kasar Gabon. ’Yan Tawayen sun tirje sai shugaba Francois Bozize ya sauka daga karagar mulki tare neman Kotun ICC ta gurfanar da shi.

shugaban 'Yan tawayen Afrika ta tsakiya Michel Am-Nondokro Djotodia a gefen hagu lokacin da suke zaman tattaunawa da Gwamnati à Libreville
shugaban 'Yan tawayen Afrika ta tsakiya Michel Am-Nondokro Djotodia a gefen hagu lokacin da suke zaman tattaunawa da Gwamnati à Libreville REUTERS/Levis Boussougou
Talla

Mai magana da yawun ‘Yan Tawayen, Florian Ndjadder, yace babu tantama saukar shugaban ne kawai zai kai ga samun zaman lafiya, yana mai cewa shugaban ne matsalar rikicin kasar.

A nasa bangaren Shugaba Bozize yace babu abinda zai sa ya sauka daga kujerar shi, yana mai zargin ‘Yan Tawayen ba Yan kasar ba ne.

Tun a watan jiya ne ‘Yan tawayen na Seleka ke ke kai hare hare a sassan yankunan Afrika ta tsakiya tare da karbe ikon manyan biranen kasar.

Sai dai kuma tun fara zaman tattaunawar tsakanin ‘Yan tawayen da Gwamnati babu wata matsaya da suka cim ma.

‘Yan tawayen sun zargi shugaban da aikata laifukan yaki da keta hakkin bil’adama, akan haka ne kuma suka bukaci kotun duniya ta ICC ta gurfanar da shugaban a gabanta.

Taron tattaunawar wanda ya shafi bangarorin Afrika ta Tsakiya guda Uku da suka hada da Gwamnati da ‘Yan tawaye da kuma ‘Yan adawa, akwai kuma wakilan ECOWAS da ke shiga tsakani.

Taron dai ya mayar da hankali ne akan yarjejeniyar da bangaren Gwamnati da ‘Yan tawayen suka amince da ita a a shekarar 2007 da 2011 inda ‘Yan tawayen suka ce Shugaba Bozize ya ki aiwatarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.