Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Faransa ba ta tabbatar da mutuwar kwamandan Alqa'ida Abu Zeid ba

Ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance gaskiyar labarin da ke cewa an kashe babban kwamandan reshen kungiyar Alqa’ida a yankin Magreb wanda sojan Faransa suka ce sun hallaka a wani farmaki da suka kai a Arewacin Mali.

La zone des opérations des armées mauritanienne et malienne contre l'Aqmi.
La zone des opérations des armées mauritanienne et malienne contre l'Aqmi. © RFI
Talla

Wata tashar talabijin a kasar Aljeriya mai suna Ennahar ce ta soma bayar da labarin kashe Abdelhamid Abou Zeid tare da wasu mutane 40 a kasar ta Mali, to sai dai shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bukaci da a yi taka-tsantsan dangane da wannan labari saboda har yanzu ba ya da tabbas.
Shi ma dai kakakin gwamnatin Faransa Najat Vallaud-belkacen ya bayyanawa tashar talabijin ta France 2 cewa, sojan kasar na ci gaba da kai mummunan farmaki a arewacin Mali, to sai dai ba ya da tabbas a game da labarin kashe kwamandan na Alqa’ida a yankin Magreb.
Majiyoyi dai sun bayyana cewa tuni hukumomin kasar Aljeriya suka soma gudanar da bincike a kan gawar wanda ake zaton cewa shugaban kungiyar ta AQMI ne, yayin da wata majiya ta kusa da gwamnatin Amurka ke cewa akwai alamun gaskiya a game da wannan batu, kuma kashe shi zai kasance babban komabaya ga wannan kungiya idan dai har ya tabbata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.