Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Kerry na Amurka ya gana da Shugaban Faransa game da rikicin Mali da Syria

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya gana da Shugaban Faransa Francois Hollande a birnin Paris inda suka tattaunawa batutuwan da suka shafi rikicin Mali da Syria a ziyarar da Kerry ke yi a kasashen Turai.

Shugaban Faransa François Hollande yana gaisawa da John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka a fadar Elysée
Shugaban Faransa François Hollande yana gaisawa da John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka a fadar Elysée REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

John Kerry wanda ya yi jinjina ga nasarar yakin Faransa a Mali, ana sa ran zai gana da ministan harakokin waje Laurent Fabius kafin ya mika zuwa Birnin Rome inda za’a gudanar da taron kawayen Syria domin fito da hanyoyin wareware rikicin kasar da ya lakume rayukan mutane sama da 70,000.

Mista Kerry ya kai ziyara Biranen London da Barlin kafin ya yada zango a Paris wanda wannan ce ziyararsa ta farko a kasashen Turai bayan ya gaji Hillary Clinton a matsayin Sakataren Harakokin wajen Amurka.

John Kerry ya alakanta Mayakan Mali da kungiyar Al Qaeda a rashen Maghrib wanda yace suna da danganta mai karfi, kuma hakan yasa Amurka ta bayar da tallafin kudi domin kakkabe mayakan a kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.