Isa ga babban shafi
Chadi-Mali-ECOWAS

Chadi ta yi kiran a gaggauta tura dakarun ECOWAS zuwa Mali

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya yi kira a gaggauta aikawa da dakarun kungiyar ECOWAS zuwa Mali domin taimakawa wajen kakkabe ‘Yan tawaye a arewacin kasar. Shugaban yace akwai bukatar a cika alkawali.

Les présidents tchadien et nigérian Goodluck Jonathan et Idriss Déby, lors d'une précédente rencontre, à Yamoussoukro
Les présidents tchadien et nigérian Goodluck Jonathan et Idriss Déby, lors d'une précédente rencontre, à Yamoussoukro REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Dakarun kasar Chadi sama da 2,000 ne ke yaki a Mali kuma shugaban kasar ya yi kira ga ECOWAS ta gaggaunata aikawa da dakarunta zuwa yankunan da aka kwato domin tafiyar da tsaro a kasar.

Dakarun kasar Chadi ne a sahun gaba saboda kwarewarsu a yaki cikin Sahara tun bayan da Faransa ta kaddamar da yaki domin kwato yankin arewacin Mali daga hannun ‘Yan tawaye.

Yanzu haka an kakkabe ‘Yan tawayen Mali daga manyan biranen Yankin Arewacin amma akwai barazanar harin kunar bakin wake da ‘Yan tawayen ke kai wa a kasar.

Tun fara yaki a Mali, kungiyar ECOWAS ta yi alkawalin aikawa da dakaru 8,000 domin yaki a kasar.

Shugaban Cote d’Ivoire kuma shugaban ECOWAS, Alassane Ouattara, yace kungiyar ta aika da wasu dakaru zuwa kasar Mali amma akwai kudi da kungiyar ke bukata domin aikawa da sauran dakarun.

A watan jiya kasashen Duniya suka yi alkawalin taimakawa da kudi sama da Dala dubu dari hudu da hamsin da biyar a Mali amma Ouattara, yace suna bukatar kudi Dala dubu dari tara da hamsin domin kaddamar da yaki a kasar Mali.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Sakatare Janar Ban Ki Moon da ya gabatar da rahoto kan yiwuwar kafa rundunar samar da zaman lafiya a kasar Mali.

Jakadan Faransa a Kwamitin, Gerard Araud, yace suna bukatar rahotan kafin karshen watan Maris mai zuwa, saboda shirin kasar na janye dakarunta daga Mali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.