Isa ga babban shafi
Tunisia

Jam’iyun siyasan Tunisiya na tattaunawa akan sabon kundin tsarin mulki

Jam’iyun siyasa a kasar Tunisiya na tattaunawa akan yadda za’ a shawo kan matsalolin kasar da kuma yadda za a samar da sabon kundin tsarin mulki a kasar. Taron tattaunawan, ya samu halartar Firaministan kasar, Hamadi Jebali da shugaban kasar, Moncef Marzouki. 

Wani gangamin taron 'Yan kasar Tunisiya a lokacin juyin -juya halin da aka yi a kasar.
Wani gangamin taron 'Yan kasar Tunisiya a lokacin juyin -juya halin da aka yi a kasar. (REUTERS)
Talla

Kungiyar ‘Yan kasuwar kasar Tunisiya ne suka shirya taron wanda har ila yau ya samu halartar kungiyoyin siyasa a kasar fiye da 40, sai dai manyan jam’iyun kasar sun kauracewa taron.

Taron dai an shirya shi ne bayan jam’iyun hadin kai guda uku sun bayyan cewa sun cimma matsaya akan matsayar kasar ta fuskar siyasa.

Kamin a samar da abon kundin tsarin mulki a kasar, har an samau goyon bayan kashi biyu daga cikin kashin ukun ‘Yan majalisu wucin gadin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.