An yankewa tsohon shugaban kasar Tunisia Ben Ali hukunci daurin rai da rai
An yanke wa tsohon shugaban kasar Tunisia hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, saboda hannu a kisan ‘Yan kasar 43, da suka yi zanga zanga da ta kifar da gwamantin shi, a shekarar da ta gabata. An yanke wa Zine El Abidine Ben Ali hukuncin ne a bayan idon shi, inda kuma aka yanke wa tsohon babban dogarin shi, Janar Ali Seriati, hukuncin daurin shekaru 20.
Wallafawa ranar:
Shi ma tsohon ministan harkokin cikin gidan kasar, Rafik Belhaj Kacem zai kwashe shekaru 15 a gidan yari.
Sai dai iyalan wadanda aka kashe a zanga zanga sun nuna fushinsu da hukuncin da aka wa Serieati da kuma Kacem inda su ke cewa an yi musu sassauci.
A nasu fadin, kamata ya yi a ce duk a yanke musu hukuncin daurin rai da rai domin ‘Yayansu da aka kashe ba kiyashi ba ne.
Akalla mutane 300 aka kashe a lokacin zanga zanga a kasar ta Tunisia wanda ya yi sandiyyar hambare gwamnatin Ben Ali inda ya nema mafaka kasar Saudi Arabia A watan Janairun bara.
An yankewa Ben Ali shekaru sama da 66 a shari’oi uku da aka gudanar inda aka tuhumeshi da laifukan badakala da kudin kasa, mallakar makamai da miyagun kwayoyi da sauransu.
Tun hambare gwamnatin Ben Ali, Tunisia ta dauki tafarkin demokradiyya a inda ta gudanar da zaben da ya bawa Jami’yar Islama ta Ennhda damar ta ke mallakar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu