Isa ga babban shafi
Tunisia

Mata sun yi zanga-zanga a Tunisia

Daruruwan mata ne suka fito saman tituna a kasar Tunisia domin adawa da kawo sauye sauyen Musulunci a Kundin tsarin mulkin kasar. Matan sun ce sabon tsarin zai keta hakkinsu.Kimanin mata 6,000 ne suka fito zanga zangar bayan sabuwar majalisa ta sauya kundin tsarin mulkin kasar zuwa tsarin musulunci.

Mata Masu zanga-zanga a kasar Tunisia
Mata Masu zanga-zanga a kasar Tunisia REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Akwai dai matsin lamba da Jam’iyya mai mulki ta Ennahda ke fuskanta daga sauran Jam’iyyun ‘Yan uwa musulmi wadanda ke kokarin ganin an tabbatar da Shari’ar Musulunci a Tunisia.

Jam’iyyar Ennahda ce ta lashe zabe a Tunisia bayan kifar da gwamnatin Zine al-Abidine Ben Ali wanda ya haramtawa Jam’iyyar shiga zabe. Bayan samun nasara ne Jam’iyar ta kulla kawance da Sauran Jam’iyyun musulunci domin tafiyar da gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.