Isa ga babban shafi
Nijar-Faransa

Wata kungiyar Farin kaya ta nemi kamfani Areva ya biya ‘Yan Nijar diyya

Wata Kungiyar fararen hula a Jamhuriyar Nijar, ta bukaci kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a kasar, biyan kudaden Diyya ga ‘Yan Nijar dai dai da yadda Kamfanin ke biyan Faransawan da suka mutu.

kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a Yankin Arlit a Jamhuriyyar Nijar
kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a Yankin Arlit a Jamhuriyyar Nijar AFP/Pierre Verdy
Talla

Wannan kuma ya biyo bayan hukunci wata kotu a Melun, inda ta bukaci kamfanin ya biya iyalan wani ma’aikaci Serge Venel, Euro 200,000 bayan ya mutu sanadiyar cutar sankara, amma Shugaban wata kungiyar Farin kaya ta Rotab Nijar, Ali Idrissa, yace kudin bai kai adadin biyan kudaden diyya ba.

A cewar Idirissa ya dace a kamanta adalci wajen biyan kudin diyya ga ma’aikatan kamfanin da ba ‘Yan kasar Faransa ba saboda yadda suke mutuwa dalilin shakar tururin Nukiliya.

Kamfanin Faransa yana cikin manyan kamfanoni masu hako Uranium sama da shekaru 40, kuma yanzu ya kafa cibiya a arewacin birnin Yamai da Arlit da Akokan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.