Isa ga babban shafi
Nijar-Najeriya-Chadi

Kasashen raya tabkin Chadi zasu samar da dakarun hadin gwiwa don yaki da Ta’addanci

Manyan Jami’an tsaron kasashen da ke raya tafkin Chadi, sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar, don nazarin hanyoyin da zasu dakile safarar makamai da kuma ayyukan ta’adanci domin samun ci gaban kasashensu.

Garken Rakuma suna sha ruwa a gabar Tabkin Chadi da ke kewaye da tsaunuka
Garken Rakuma suna sha ruwa a gabar Tabkin Chadi da ke kewaye da tsaunuka Getty Images
Talla

Dakta Bello Muhammed Halliru Ministan tsaron Najeriya yace Nijar da Chadi da Najeriya sun hade kansu domin kare iyakokinsu wajen dakile shigo da makamai.

A cewar Dakta Bello suna neman hadin kan kasar Kamaru da Afrika ta tsakiya domin samar da Sojin hadin gwiwa.

Dakta Bello yace akwai barazanar Fasa kwabrin makamai da ake shigowa da su ta iyakokin kasasashen da kuma ayyukan ta’addanci da suka addabi Najeriya.

A kwanan baya ne Gwamnatin kasar Chadi ta yi kiran kasashen 16 da ke kungiyar raya tafkin Chadi domin samar da dakarun hadin kai don yaki da ‘Yan kungiyar Boko Haram da ke barazana ga sha'anin tsaro a Najeriya da makwabtanta.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a taron kungiyar da aka gudanar a birnin Libreville na kasar Gabon.

A cewar Shugaban ya zama wajibi mambobin kasashe 16 masu ruwa da tsaki game da tafkin Chadi, su kafa Dakarun hadin gwiwa, domin yaki da Ta’addanci.

Mista Deby Yace illar rikicin Boko Haram a Najeriya, tafi ta tafkin Chadi.

Deby ya samu goyon bayan Shugaban kasar Tsakiyar Africa Francois Bozize, wanda yace zai bada gudunmawar Dakarun kasarsa domin samar da Dakarun hadin kan.

Taron kungiyar kasashen yana da niyyar farfado da tafkin Chadi ne, wanda dimbin jama’a ke dogaro da shi don rayuwa.

Kungiyar Raya Tafkin Chadin ta kunshi Kamaru da Jamhuriyar Tsakiyar Africa da Chad da Libya da Nijar da Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.