Isa ga babban shafi
Afrika-Bankin Duniya

Bankin Duniya yace an samu ci gaba a kasashen Yamma da Sahara

Babban Bankin Duniya yace tattalin Arzikin kasashen yammacin Afrika ya samu ci gaba bana. Wannan na zuwa ne saboda samun rangwame ga farashin kaya da yawaitar hannayen jari da hako ma’adanai da suka kawar da raunin fitar da kaya zuwa waje.

Wani sanye da Rawani a yankin Timbuktu a kasar Mali
Wani sanye da Rawani a yankin Timbuktu a kasar Mali Reuters
Talla

A rehoton da Babban Bankin ya ke fitarwa kan tattalin arzikin Nahiyar Afrika a kowace shekara, Bankin ya yi hasashen habakar tattalin arzikin kasashen Afrika daga kashi 5.2 a bana sabanin bara da aka samu kashi 4.9.

Mataimakiyar shugaba a babban Bankin ta yankin Afrika Obiageli Ezekwesili, tace tattalin Arzikin kasashen Afrika na sake daidaituwa, abinda yasa ya ke saurin habaka.

Sai dai duk da hakan inji Babban Bankin ba a yabon dan Kuturu domin kasantuwar akwai matsalar karancin abinci a yankin, sakamakon yadda har yanzu kashi 25 na Abincin daya kamata kasashen su yi amfani da shi, shi ne suke samarwa.

Don haka Bankin ya nuna damuwa akan yiyuwar yaduwar karancin abinci a kasashe kamar Senegal, Kamaru, da kuma yankin arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.