Isa ga babban shafi
Senegal

Hukumar zaben Senegal ta tabbatar da za ayi zaben Shugaban kasa zagaye na biyu

Jagoran 'yan adawan kasar Senegal, Macky Sall, na yunkurin hada kan 'yan adawan, dan fafatawa da shugaba Abdoulaye Wade, a zabe zagaye na biyu da za’ayi ranar 18 ga wannan wata.Wakilan kungiyar M23 dake adawa da shugaba Wade, na cigaba da tattaunawa dan marawa Sall baya, ganin cewa shi ya zo na biyu, a zaben. 

Shugaban Senegal Abdoulaye Wade da tsohon PM Macky Sall
Shugaban Senegal Abdoulaye Wade da tsohon PM Macky Sall Photo : Reuters/Montage : RFI
Talla

Yan adawan kasar ta Senegal nata neman hadewa domin kawar da Shugaba Abdoullaye Wade daga zarcewa wa'adi na uku a zagaye na biyu na zaben kasar da za ayi ranar 18 ga wannan watan.

Hukumar zaben kasar ta ce shugaba Abdoulaye Wade dan shekaru 85 da haihuwa, zai fafata da Tsohon Fira Ministansa, Macky Sall, a zaben shugaban kasa zagaye na biyu, da za’ayi ranar 18 ko kuma 25 ga watan nan.

Hukumar ta ce shugaba Wade ya samu kashi 35 cikin 100 na kuri’un, yayin da Sally ya samu kashi 27 cikin 100, sai kuma Mustapha Niasse mai kashi 13.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.