Isa ga babban shafi
Senegal

'Yan kasar Senegal na zaman jirar sakamakon zaben Shugaba kasa

Yanzu haka ana ci gaba da jiran sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi jiya Lahadi a Senegal, inda shugaba Abdoulaye Wade ke fafatawa masu neman ganin sun hana shi komawa karagar mulki.

© AFP/Seyllou
Talla

Mai Shiga tsakani na kungiyar kasashen Afrika ta AU, a zaben kasar ta Senegal, kuma Tsohon shugaban Nigeria, Olusegun Obasanjo, ya sake jaddada kiran san a ganin an kaucewa jefa kasar cikin tashin hankali.

Mutane sun kwashe dare tare da wayewar gari na saurarar kafofin yada labarai, domin sanin wanda ke kan gaba tsakanin 'yan takara 14 da suka hada da Shugaba Wade, wanda mutane suka yi masa shewa na gwalewa, yayin da ya kada kuri'a.

Muddun zaben ya kai zagaye na biyu, idan babu wanda ya samu nasara kai tsaye, 'yan adawa zasu kungule, su yi gangamin karshe na kawar da Shugaba Abdoulaye Wade dan shekaru 85 da haihuwa, daga madafun ikon kasar da ke yankin Yammacin Nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.