Isa ga babban shafi
Senegal

Alamu suna tabbatar da cewa zaben Shugaban Senegal ya kai zagaye na biyu

Sakamakon farko na hukumar zaben kasar Senegal, ya yuwuwar tafiya zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa cikin tsakiyar watan Maris.Tunda faru, Shugaban Kasar ta Senegal, Abdoulaye Wade, ya ce akwai fatar cewa ana iya zuwa zabe zagaye na biyu a kasar, saboda sakamakon farko na wasu sassa ya nuna cewar, ya samu kashi 32, yayin da Macky Sall ya samu kashi 25.

Shugaban Senegal mai barin gado Abdoulaye Wade yayin taron manema labarai
Shugaban Senegal mai barin gado Abdoulaye Wade yayin taron manema labarai RFI/Anthony Ravera
Talla

Jakadar Kungiyar kasashen Afrika na musamman a zaben kasar ta Senegal, kuma Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce shugaba Abdoulaye Wade zai amince da sakamakon zaben koda ya sha kaye inda ya ce shugaba Wade a matsayin sa na mai girmama demokradiya, ya gabatar da kansa a zabe, kuma idan mutane sun yanke hukunci, dole ya amince da haka, mutane na cewa, ba zai amince ba, wannan ba haka bane, saboda ba dalilin hakan.

Tsohon Macky Sall dake kalubalantar Shugaba Wade
Tsohon Macky Sall dake kalubalantar Shugaba Wade RFI/Laurent Correau

Tsohon PM Sall ya ce duk sakamakon da suka samu na nuni da tafiya zagaye na biyu na zaben tsakaninsa da Shugaba Wade wanda farin jininsa ya sukurkuce, saboda neman zabe karo na uku, bayan mulki shekaru 12, dukda kyara da aka yi wa kundin tsarin mulki aka takaita wa'adi biyu wa mukamun shugaban kasa.

Muddun aka rasa dan takarar shugaban kasa da ya samu fiye da kashi 50 cikin 100, tilas a tafi zagaye na biyu tsakanin manyan 'yan takara biyu, kuma za ayi zaben ranar 18 ga watan Maris ko kuma ranar 1 ga watan Afrilu mai zuwa.

Akalla mutane shida sun hallaka cikin kwanakin da aka shafe ana zanga zanga kan takarar Shugaba Wade.

Senegal ta kasance kalilan daga cikin kasashen anhiyar Afrika da sojoji basu taba kwace madafun ikon kasar ba, tun bayan samun 'yanci daga Turawan mulkin mallamakn kasar Faransa cikin shekarar 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.