Isa ga babban shafi
Libya

Libya zata tura ‘Yantawaye horon soji zuwa Jordan

Kasar Libya tace zata tura tsofaffin ‘yan tawayen da suka yaki tsohon shugaban kasar Kanal Ghaddafi, su dubu 10 zuwa kasar Jordan don samun horon da zai taimaka a shigar da su aikin Soji a kasar.A cewar kakakin ma’aikatar cikin gidan kasar, Janar Abdelmonem al-Tunsi, akwai yarjejeniya da kasar Libya ta kulla da kasar Jordan domin bayar da horo ga ‘yan kasar 10,000.

'Yan tawayen Libya
'Yan tawayen Libya Reuters
Talla

Wata Takardar yarjejeniyar da kamfanin Dillacin Labaran AFP ya samu, an bayyana cewa a farkon watan Mayu ne ‘Yantawayen kimanin 1,000 zasu fara karbar horo a Jordan kafin tura wasu 2,000.

Tutar Kasar Libya
Tutar Kasar Libya

Mista Tunsi yace sun yanke shawarar kulla kawance da Jordan ne saboda kwarewarta wajen aikin horar da ‘Yan sandan kasar Iraqi.

Yanzu haka kuma ma’aikatar cikin gidan ta fara karbar takardun makarantar ‘Yantawayen domin samun shiga shirin horon aikin soji.

‘Yantawayen dai sune suka kwashe watanni suna yaki da dakarun Kanal Ghaddafi tare da samar da tsaro a kasar Libya kafin kashe Ghaddafi a Octoban bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.