Isa ga babban shafi
Libya

An yi arangama tsakanin ‘Yantawayen Libya a kudancin Tripoli

Hukumomin Kasar Libya sun ce an samu arangama tsakanin bangarorin ‘Yan Tawayen kasar da basa ga maciji, abinda ke ci gaba da fito da fargaba a kan halin da kasar ta samu kanta a ciki, bayan kawar Tsohon shugaban kasa, Muammar Ghadafi.

Wasu Jami'an kiwon Lafiya da dakarun Libya suna kokarin daukar wadanda suka ji rauni a Asibitin birnin Gharyan kusa da Birnin Tripoli
Wasu Jami'an kiwon Lafiya da dakarun Libya suna kokarin daukar wadanda suka ji rauni a Asibitin birnin Gharyan kusa da Birnin Tripoli REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Tutar Kasar Libya
Tutar Kasar Libya

Wani jami’I a ofishin Fira Minista Abdurahim al Kib, yace an samu tashin hankalin ne a garin Gharyan, da ke da nisan kilomita 80 daga Tripoli, amma ya zuwa yanzu babu adadin wadanda suka samu raunuka.

Sai dai wata majiya daga Jami’an tsaron kasar na cewa rikicin ya barke ne bayan da wani mazauni birnin Assabia ya kashe wani mutum a yankin Gharyan.

Majiyar tace mutane biyu sun mutu kuma akalla mutane 39 suka jikkata tun barkewar rikicin a ranar Assabar.

Tun bayan kifar da gwamnatin Gaddafi, ake samun Rikici tsakanin ‘Yantawaye bayan sun ki hannunta muggan makaman da suka mallaka.

Ko a farkon watan Janairu an yi musayar wuta a birnin Tripoli, lokacin da ‘yan bindiga daga Misrata suka yi arangama da ‘Yantawaye inda aka samu mutuwar mutane hudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.