Isa ga babban shafi
Rasha-Libya

Rasha ta bukaci binciken NATO game da rikicin Libya

Gwamnatin kasar Rasha ta sake bayyana bukatar ta na ganin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, ta yi bayani kan yadda ta kashe fararen hula a hare haren da ta kai kasar Libya, domin kawar Tsohon shugaban kasa, Muammar Ghadafi.

Jekadan Faransa  Alain Juppe a bangaren hagu yana gaisawa da Jekadan kasar Rasha Vitaly Churkin  a lokacin taron kwamitin Sulhu na Majalisar Dunkin Duniya
Jekadan Faransa Alain Juppe a bangaren hagu yana gaisawa da Jekadan kasar Rasha Vitaly Churkin a lokacin taron kwamitin Sulhu na Majalisar Dunkin Duniya REUTERS/Jessica Rinaldi
Talla

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vitaly Churkin, yace zai kalubalanci zaman kwamitin Sulhu a cikin wanna makon, bayan wani rahoto da Jaridar New York Times ta buga a kasar Amurka, cewa NATO ta kashe fararen hula tsakanin 40 – 70, tare da Sukar Ban Ki-moon wanda ya nuna goyon bayan kai haren haren NATO.

Matakin kaddamar da yaki da kasashen Birtaniya da Faransa da Amurka suka yi a kasar Libya ya raba kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya gida biyu.

Kasashen Rasha da China da Brazil da Afrika ta Kudu sune kasashen da suka karacewa kada kuri’ar amincewa da matakin kaddamar da yaki kan Libya domin kare fararen hula. Inda daga bisani suka zargin NATO wajen wuce gona da iri da har ya yi sanadiyar kisan Gaddafi.

A makon daya gabata Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana cewa NATO sun aiwatar da yakinsu ba tare da keta ka’idojin Majalisar ba.

A ranar Alhamis Jekadan kasar Rasha yace zai yi kokarin gabatar wannan zance a gaban kwamitin Sulhu domin daukar mataki akan NATO.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.