Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Jami’an tsaro sun kashe mutane 24 a Congo, inji HRW

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Right watch tace jami’an tsaro a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun kashe mutane 24 kafin rantsar da Joseph Kabila wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Magoya bayan Jam'iyyar adawa ta UDPS lokacin da suke gudun tsira bayan harba masu hayaki mai sa hawaye a birnin Kinsasha
Magoya bayan Jam'iyyar adawa ta UDPS lokacin da suke gudun tsira bayan harba masu hayaki mai sa hawaye a birnin Kinsasha REUTERS/Finbarr O"Reilly
Talla

A cewar kungiyar, an kashe mutanen ne a Kisasha babban birnin kasar inda madugun adawa Etienne Tshisekedi ke da rinjaye.

Cikin wadanda suka mutu har da wata mata mai shekaru 21 da aka harba tare da danta mai shekaru 8 na haihuwa a ranar  da aka bayyana sakamakon zabe.

Kungiyar Human Right tace ‘yan sanda sun yi kokarin sakaye gawawwakin mamatan, amma ta tabbatar da adadin wadanda suka mutu ne bisa binciken da ta gudanar da kisan da aka gudanar a idon jami’anta.

Har yanzu dai gwamnatin kasar bata mayar da martani ba kan wannan zargin.

A ranar 9 ga watan Disemba ne hukumar zabe ta bada sakamakon zaben inda aka bayyana shugaba Kabila a matsayin wanda ya lashe zaben da rinjayen kuri’u kashi 49, abokin hamayyarsa kuma Tshisekedi aka bayyana ya samu kuri’u kashi 32.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.