Isa ga babban shafi
Turai-Amurka

Trump ya sake barazanar kakabawa motocin Turai sabbin haraji

Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kakaba Kudaden Haraji na musamman kan motoci da sauran ababen hawa da kasashen Turai ke shigarwa Amurka, muddin ya gaza cimma yarjejeniya daidaita cinikayya tsakaninsa da kungiyar kasashen Turan EU.

Tun a shekarar bara Amurka ta kakaba Karin haraji kan karafa da aluminium da kasashen Turai ke shigarwa kasuwanninta
Tun a shekarar bara Amurka ta kakaba Karin haraji kan karafa da aluminium da kasashen Turai ke shigarwa kasuwanninta Kevin Lamarque / Reuters
Talla

Sabunta barazanar kakabawa motoci da sauran ababen hawan da kasashen Turan ke shigarwa kasuwannin Amurka, ya zo ne kwanaki 2, bayanda ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar ta wallafa rahoton cewa, motocin da kasashen Turan ke kaiwa Amurka na tattare da barazana ga tsaron kasar.

Bayyanar rahoton dai ka iya sa gwamnatin Donald Trump ta aiwatar da barazanar kakaba harajin kasha 25 kan motocin turai da sauran ababen hawan da suke kerawa, nan da watanni 3.

Sabon harajin dai zai fi shafar Jamus, wadda Amurka ta ce motocin da take kerawa na cutar da kamfanoninta na cikin dake kera ababen hawan.

Sai dai kungiyar kasashen Turan EU ta gargadi Amurka da cewa za ta maida martanin kakaba nata harajin kan kayyakin da Amurka ke shigarwa kasuwanninta.

Tun a shekarar bara Amurka ta kakaba Karin haraji kan karafa da aluminium da kasashenTurai ke shigarwa kasuwanninta, daga bisani aka cimma matsaya tsakaninta da EU a watan Yulin na shekarar bara, sai dai a baya bayan nan shugaba Trump ya nuna rashin gamsuwa da yadda tattaunawa tsakaninsu ke gudana kan huldar kasuwancin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.