Isa ga babban shafi
Amurka-China

Amurka ta kara lafta wa China haraji kan Dala 200bn

Shugaban Amurka Donald Trump ya zafafa takaddamar yakin kasuwanci tsakaninsa da China, in da ya lafta wa kasar haraji kan kayayyakin da kudinsu ya kai Dala biliyan 200, sannan ya yi barazanar sake lafta harajin muddin China ta yi gigin mayar da martani.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria
Talla

Trump ya ce, China ta ki sauya wasu matakanta na rashin adalci da ke cutar da ma’aikata da kuma harkokin kasuwancin Amurka, abin da shugaban ke cewa hakan na barazana ga tattalin arzikinsu.

Sabbin matakan harajin za su fara aiki a ranar 24 ga watan Satumba kan na’ukan kayayyaki har kusan dubu 6 da China ke shigarwa Amurka.

Amurka za ta fara sanya harajin kashi 10 ne kan kayayyakin kafin ta rubanya zuwa kashi 25 nan da shekara mai zuwa.

Tuni China ta bakin ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta lashi takobin mayar da martani ga Amurka.

Sai da a cewar Trump, muddin China ta mayar da martanin, to babu shakka za su dauki mataki na uku mafi tsauri da zai shafi kayayyakin da kudinsu ya kai Dala biliyan 267.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.