Isa ga babban shafi
Brics

Babu mai galaba a yakin kasuwanci a duniya- Jinping

Shugaban China Xi Jinping ya ce, ba wanda zai yi galaba idan aka shiga yanayi na yaki a fagen kasuwanci tsakanin kasashen duniya. Shugaban na jawabi ne a wurin bude taron koli na kasashe 5 masu samun habakar tattalin arziki da ake kira BRICS da ke gudana yanzu haka a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Shugaban China Xi Jinping a wurin taron Brics a Johannesburg
Shugaban China Xi Jinping a wurin taron Brics a Johannesburg REUTERS/Fred Dufour/Pool
Talla

Duk da cewa bai fito fili kara ya ambaci sunan Amurka ba, to amma ko shakka babu shugaban na Sin na  gugar zana ne dangane da matakan da gwamnatin Donald Trump ke dauka kan sauran kasashen duniya a fagen kasuwanci.

Shugabannin kasashe 5 da ke samun habakar tattalin arziki a wannan zamani ne ke halartar wannan taro na Johannesburg da suka hada da Brazil da Rasha da China da India da kuma Afrika ta Kudu, in da za su share tsawon yini uku suna tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

Ko baya ga shugabannin kasashen biyar, an kuma gayyaci shugabanni na musamman daga wasu kasashe na nahiyar Afrika a matsayin manyan baki, yayin da gungun na BRICS ke ci gaba da shimfida siyasar tattalin arziki wadda ta yi hannun riga da ta kasashen yammancin duniya da Bankin Duniya da kuma IMF.

To sai dai wani abu da zai yi tasiri wajen daukan hankulan mahalarta taron na wannan karo, shi ne rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China, wanda ko shakka babu zai iya shafar wasu daga cikin manyan manufofin Brics, a matsayin China kasar da ke da dimbin jari a wannan tafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.