Isa ga babban shafi
china-afrika

China za ta bai wa Afrika dala biliyan 60

Shugaban kasar China Xi Jinping na ganawa da shugabannin kasashen Afrika 40 a taron da aka bude a yau Jumma’a a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu domin tattaunawa game da bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Afika da China.

An gudanar da irin wannan taron tsakanin China da Afrika a birnin Beijing a shekara ta 2000.
An gudanar da irin wannan taron tsakanin China da Afrika a birnin Beijing a shekara ta 2000. REUTERS/Jason Lee
Talla

Shugaba Jinping ya bayyana cewa kasarsa za ta bai wa Afrika tallafin dalar Amurka biliyan 60 da ya hada da kudin aro, lamarin da ke nuna irin dukufar da China ta yi wajan raya kasashen Afrika.

Tattalin arzikin China ya yi kasa a ‘yan kwanakin nan, abinda ya haifar da faduwar farashin kayayyaki a sassa dabam dabam na duniya yayin da kasar ta China ta rage yawan hannayen jarinta a Afrika fiye da kashi 40 cikin 100 a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar.

A karo na biyu kenan tun shekara ta 2000 a Beijing da China ta hada shugabannin Afrika wuri guda domin gudanar da irin wannan taron mai taken FOCAC

Tuni dai Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sanar da kulla yarjejeniyar dala miliyan 6.5 da China a fanin ma’adanai da yawon bude ido.

Shi ma dai shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya ce zai yi amfani da wannan damar wajen neman taimakon China a fanin wutar lantarki da kwangilar hanyar sufurin jiragen kasa da manyan tittuna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.