Isa ga babban shafi
Duniya

Za a soma babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan birnin Quds

Bayan watsin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi da daftarin da Masar ta gabatar da ke neman hana Amurka ayyana Quds a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila, a gobe Alhamis za a soma zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya wanda babu damar hawan kujerar na-ki zai tattauna a kan wannan batu.

Kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya
Kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya
Talla

Kasashen Turkiyya da Yemen ne suka bukaci kasashe 193 su tafka mahawara kan wannan batu a gobe Alhamis, to sai dai Amurka ta yi gargadin cewa za ta tantance tare da sanin irin zaman da za ta yi da kasashen da suka amince da hakan a gobe.

Shugaba Trump ya ce Isra'ila kasa ce mai ‘yanci saboda haka tana iya sanya babban birnin ta inda ta ke so.

Trump ya ce matakin ba zai sauya matsayin Amurka na samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba idan sun amince a tsakanin su.

Tuni wannan batu na Mista Trump ya janyo suka daga shugabannin duniya daban-daban.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Alla-wadai da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka, inda ya ke cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.