Isa ga babban shafi
MDD

Fatan sabon sakatare janar na Majalisar dinkin duniya shine duniya ta samun lafiya a 2017

Sabon magatakardan MDD Antonio Guterres ya ce fatansa shi ne shekara ta 2017 ta kasance ta zaman lafiya ga duniya baki daya kamar yadda ya sanar a sakonsa na shiga sabuwar shekarar. 

shugaban majalisar dinkin duniya Antonio Guterres
shugaban majalisar dinkin duniya Antonio Guterres
Talla

Guterres wanda ya gaji Ban Ki-moon a yau daya ga watan anairu , ya fara aikin ne a cikin yanayi na rashin zaman lafiya da ake fuskanta a sassan duniya da dama musamman a kasashen Syria, Libya, Yemen, Sudan ta Kudu da dai sauransu.

Babu shakka akwai jan aiki a gaban Guterres, lura da yadda duniyar ta rude musaman rawar da ya kamata majalisar ta taka, a daidai lokacin da manyan kasashen duniya ke nuna kamar ba da gaske suke yi ba, wajen magance matsalolin da duniya ke fama da su, musaman rikice rikicen dake wakana a kasashen gabas ta tsakkiya.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.