Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya yi watsi da zargin cin zarafin mata

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi watsi da zargin da wasu mata uku suka ma sa na cewa yaci zarafin su, in da suka buƙaci Majalisar kasar ta ƙaddamar da bincike a kai.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Rachael Crook, wadda ta yi aiki a ginin Trump Tower mallakin shugaban, ta zarge shi da tirsasa ma ta wajen sumbatar ta a baki a shekarar 2005.

Ɗaya daga cikin matan, Samantha Holvey yayin ganawa da manema labarai ta ce, a matsayinsu na mutanen da ba a san su ba, fitowa su yi irin wannan zargi abu ne mai wahala.

Shugaba Trump ya zargi mambobin Jam’iyyar Democrat da kitsa labarain ganin cewar, sun kasa tabbatar da zargin da suke yi ma sa na hada kai da Rasha wajen samun nasarar zabe.

Ƴan Majalisar Dattawa uku da suka hada da Sanata Bernie Sanders da Cory Booker da Jeff Merkley sun buƙaci shugaban ya sauka daga muƙaminsa saboda zargin.

Shugaba Trump ya gamu da irin waɗannan zarge-zarge lokacin yaƙin neman zaɓensa, in da mata suka yi ta zargin cewa ya ci zarafin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.