Isa ga babban shafi
Amurka

Matan da ke zargin Trump na son a hukunta shi

Wasu mata guda uku da ke zargin shugaban Amurka Donald Trump da cin zarafin su, sun buƙaci majalisar dokokin ƙasar da ta gudanar da bincike domin hukunta shi.

Rachel Crooks, Jessica Leeds da Samantha Holvey na bukatar majalisa ta bincika zargin da suke wa Donald Trump.
Rachel Crooks, Jessica Leeds da Samantha Holvey na bukatar majalisa ta bincika zargin da suke wa Donald Trump. REUTERS/Andrew Kelly
Talla

Ɗaya daga cikin matan, Samantha Holvey yayin ganawa da manema labarai, ta ce a matsayin su na mutanen da ba a san su ba, fitowa su yi irin wannan zargi abu ne mai wahala.

Ya zuwa yanzu mata 13 suka zargi shugaban na Amurka da cin zarafin su.

Shugaba Trump ya gamu da irin waɗannan zarge-zarge lokacin yaƙin neman zaɓen sa, inda mata suka yi ta zargin cewa ya ci zarafin su.

Wasu ƴan majalisar dattawa uku Sanata Bernie Sanders da Cory Booker da Jeff Merkley sun buƙaci shugaban ya sauka daga muƙamin sa saboda zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.