Isa ga babban shafi
MDD-Norway

Norway ce ta fi kowa farin ciki a duniya-MDD

Yau ce ranar da Majalisar dinkin duniya ta kebe a matsayin ranar farin ciki ta duniya. Kuma a rahotan da ta fitar, Norway ce ta fi kowacce kasa farin ciki a duniya. China kuma ta shafe sama da shekaru 25 cikin bakin ciki.

Norway ta fi kowa farin ciki a duniya in Majalisar Dinkin Duniya
Norway ta fi kowa farin ciki a duniya in Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Romeo Ranoco
Talla

Rahotan Majalisar Dinkin Duniya kan ranar farin ciki ta duniya, ya bayyana Norway da ke mataki na hudu a shekarar da ta gabata zuwa matsayi na farko.

Sauran kasashen da ke bi mata sun hada da Denmark a matsayi na 2, sai Iceland na 3 da Switzerland na 4.

Wadanan kasashen da aka bayyana a sahun farko anyi amfani da kulawa da ‘yanci da kyautatawa da amana da lafiya da kudadde shiga da tsarin gwamnati mai kyau wajen kai su wannan matsayi.

Sauran kasashen kuma bayan wadanan 4, akwai Finland a mataki na 5 a teburin Majalisar, kana akwai Netherland na 6 sai Canada na 7.

New Zealand ce ta 8, sai Australia da Sweden da ke kai da kai a matsayin na 9.

A cewar Rahotan, wadanan kasashen 10 na ciki kasashe masu tasowa a duniya, Kuma haka na tabbatar da cewa Kudi ba shi ne kadai ke kawo farin ciki a duniya ba.

Majalisar ta ce tazara tsakanin kasashen da aka Ambato da masu arziki ya zarta tunani a teburin.

Rahotan ya kuma bayyana China da ke cikin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, cewa ta shafe shekaru 25 ba ta cikin farin ciki, Kazalika kuma ya ke a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.