Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gayyaci Abbas na Falasdinu

Shugaban Amurka Donald Trump ya gayyaci shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas zuwa fadar White House bayan wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho a jiya jumma’a. 

Shugaban Falasdinu  Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas Palestinian President Office (PPO)/Handout via REUTERS
Talla

A karon farko kenan da shugabannin biyu suka gana da wayar tarho tun bayan rantsar da Trump a a ranar 20 ga watan Janairun da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya rawaito cewa, Trump ya mika wa Abbas goron gayyatar ne don tattaunawa game da yadda za a farfado da shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
 

Fadar White ta ce, shugaba Donald Trump ya yi amanna cewa, dole ne Isra'ila da Falasdinu su yi zaman keke da keke don cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.