Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na kan bakarta akan Kasar Falasdinu

Kasar Faransa ta ce goyan bayan da take da shi wajen ganin an kafa kasar Falasdinu ya zarce na kowanne lokaci a yayin da Isra’ila ke kokarin samun goyon bayan gwamnatin Trump na Amurka domin dakile ‘yancin Falasdinawa.

Shugaban Faransa François Hollande da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Faransa François Hollande da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Francois Delattre ne ya bayyana haka yayin da kasar Amurka ta sauya matsayinta dangane da shirin kafa kasar Falasdinu da za ta zauna tare da Isra’ila.

Jakadan ya ce duk da ya ke bashi da hurumin Magana da yawun wata kasa, amma matsayin Faransa bai sauya ba wajen ganin an kafa kasar Falasdinu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci daukar duk matakan da suka dace wajen ganin an kafa kasar Falasdinu sakamakon sauya matsayin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, kafin ganawa da Firaminista Benjamin Netanyahu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya fi kaunar amincewa da kasa guda idan har Isra’ila za ta samu zaman lafiya da Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.