Isa ga babban shafi
Israel-Palestine

MDD ta soki shirin Isra’ila na gini a yankin Falasdinu

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwar ta kan shirin Isra’ila na gina wasu Karin sabbin gidaje 2,500 a Yankunan Falasdinawa.

Friministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Friministan Isra'ila Benyamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Sakatare Janar Antonio Guterres ya ce samun kasar Falasdinu wajibi ne a Yankin, saboda haka daukar irin wannan mataki zagon kasa ne ga dokokin duniya

Kakakin Sakatare Janar Stephane Dujarric ya ce Guteres ya jaddada muhimmancin mutunta kudirorin Majalisar da kuma haramta gina gidajen da Isra'ila ke ci gaba da yi.

Majalisar ta bayyana goyan bayan ta ga kudirin da kwamitin Sulhu ya amince da shi a watan jiya na haramta duk wani gini da Israila ta yi, wanda a karon farko Amurka a karkashin shugaba Barack Obama taki hawa kujerar naki.

Tuni dai hukumar Gudanarwar Falasdinawa ta bukaci kasashen duniya su dauki matakin gaggawa kan Israila.

Sakatare Janar na kungiyar Falasdinawa Saeb Erakat ya yi zargin cewar Israila na daukar matakin ne saboda goyan bayan da take samu daga sabon shugaban Amurka Donald Trump.

Kasar Faransa da kawayen sun ce ya zama dole a kawo karshen gine-ginen da kuma tabbatar da kasar Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.