Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta mayar da hankali ga sukar Trump

‘Yar Takarar shugabancin Amurka a Jamhuriyar Democrat Hillary Clinton ta mayar da hankali ga suka da caccakar abokin hamayyarta Donald Trump na Republican yayin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da zaben kasar.

Hillary Clinton da ke neman shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat
Hillary Clinton da ke neman shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat REUTERS/Brian Snyder
Talla

Hillary Clinton ta koma sukar Trump ne a yakin neman zabenta yayin da take fuskantar koma-baya sakamakon sakwannin email da FBI ta ce zata sake bincike akai.

Clinton na kokarin janye hankalin Amurkawa ne daga kalubalanen da ta ke fuskanta a yanzu kan binciken FBI.

A karon farko wani sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna Donald Trump ya zarce Hillary Clinton a Jihar Florida, amma ‘yar takarar Democrat ta shaidawa magoya bayanta cewar, Trump ba shi da kwarewar da zai rike mukamin shugaban kasa.

Clinton ta ce rahotanni dabam dabam da ke nuna yadda Trump ke cin zarafin mata, da yadda ya ke saurin harzuka da kuma kaucewa biyan haraji ya nuna cewar ba shugaba ne da Amurkawa za su amince da shi ba.

Wata kuri’ar kuri’ar jin ra’ayin jama’a a Florida ya nuna cewar Clinton na iya lashe zaben Jihar da kashi 48, yayin da Trump zai samu kashi 40.

Amma kuri’ar da tashoshin ABC News da Washington Post suka gudanar ya nuna cewar Trump na da kashi 46 yayin da Clinton ta samu kashi 45.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.