Zaben Amurka ya kunyata ni- Kerry
Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry ya ce yanayin siyasar bana a Amurka ya kunyata shi tare da jefa aikin shi cikin mawuyacin hali musamman a lokacin da ya ke da'awar tabbatar da mulkin demokuradiya a wasu kasashe.
Wallafawa ranar:
Kerry ya fadi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da wasu dalibai tare da Magajin garin London a ziyarar da ya kai a Birtaniya inda ya karbi wata kyauta karramawa a Chatham house.
A cewar Kerry yanayin siyasar bana ya sa an koma ana muhawara kan batutuwan da ba su da amfani.
Mista Kerry ya ce ana ma shi wani kallo a duk lokacin da ya dauko batun bin tsarin dimokuradiya tare da wasu ministocin harakokin waje ko Firaministan wata kasa.
A ranar 8 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin Hillari Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu