An bude sauraren karar kisan Hariri na Lebanon
An bude shari’ar mutane hudu da ake zargi sun kashe Firaministan kasar Lebanon Rafiq Hariri a shekarar 2005 amma ba a gaban idon mutanen ba wadanda ake zargi kuma mayakan kungiyar Hezbollah ne.
Wallafawa ranar:
An kashe Hariri ne tare da wasu mutane sama da 20 a wani harin bam da aka kai a birnin Beirut a shekarar 2005 wanda ya raunata mutane 225.
An bude sauraren karar mutanen ne hudu da ake zargi wadanda har yanzu ba a cafke ba a kotun hukunta laifukan yaki a birnin Hague.
Tuni dai kungiyar Hezbollah ta nisanta kanta da daukar alhakin kai harin amma tace kisan Hariri minakisa ce tsakanin Isra’ila da Amurka.
A shekarar 2011 ne kotun Hague ta bayar da sammacin kamo mutanen hudu da ake zargi wadanda aka bayyana sunayensu a matsayin Mustafa Badreddine da Salim Ayyash da Hussein Oneissi da Assad Sabra dukkaninsu mambobin kungiyar Hezbollah ta mabiya Shi’a.
A ranar Masoya ne aka kashe Firaminista Hariri Dan Sunni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu