Isa ga babban shafi
Lebanon

Kotu ta samu mutum na Biyar a zargin kisan Rafeq Hariri.

Kotun sauraron korafe-korafe mai samun goyon bayan Majalisar dunkin Duniya da aka kafa domin gurfanar da makasan tsohon Piraiministan kasar Lebanon Rafiq Hariri tace ta samu wanda ake tuhuma na Biyar akan tashin Bomb din kasar Beirut. Wannan harin Bomb dai an kai shi ne a cikin Shekarar 2005.

Refeeq Hariri
Refeeq Hariri
Talla

Alkalin Kotun na wuccin-gadi ya tabbatar da samun Hassan Habib Merhi wanda aka zarga da Hannu a harin na 14 ga Watan Fabrairun 2005.

Baya ga Hassan Habib dai wasu Hudu daga cikin Mambobin Sojin sa ai na kungiyar Hezboullah na huskantar zargi akan wannan kazamin harin daya kashi Hamshakin Billionair wato Hariri da wasu mutane 22 a Beirut.

Hariri dai ya fit one daga mabiya akidar Sunni ‘yan tsiraru da kuma baya goyon bayan mamayar da kasar Siriya ke yiwa Lebanon, a yayin da ake ganin cewar Kungiyar Hizboullah ta Lebanon nada alakar kud-da-kud da hukumomin birnin Damascus.

Sai dai kungiyar ta Hizboullah ta karyata zargin da ake mata na hannu ga tashin Bomb din.

Shugaban kungiyar Hizboullah Hassan Nasrullah yayi watsi da Kotun tare da bayana ta a matsayin Karyar Farautar kasar Amurka da Israela, harma yana bayyana cewar ba zasu iya kama kowa daka cikin wadanda suka shafawa Laabu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.