Isa ga babban shafi
Syria

Kwararrun dake binciken makamai masu guba sun fice daga Syria

Bayan kwashe kwanaki hudu suna aiki, kwararrun da Majalisar Dinkin Duniya ta tura zuwa kasar Syria domin bincike akan zargin da ake yiwa Shugaba Bashar al – Assad na yin amfani da makamai masu guba akan fararen hula sun fice daga kasar.

Tawagar motocin kwararrun MDD a Syria
Tawagar motocin kwararrun MDD a Syria
Talla

Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar yau Asabar wakilan na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka sami jagorancin Ake Sellstrom suka fice daga dakunan otel dinsu dake Damascus suka tsallak zuwa cikin Lebanon dake makwabtaka da Syria.

Ana sa ran zasu mika rahoto ga Sakatare Janar Ban Ki – moon na ba da jimawa ba a dai lokacin da majalisar ke kira ga kasashen yammacin duniya da su bari a kammala bincike kamin daukan mataki akan gwamnatin Assad.

Rahotanni na kara da cewa, Amurka ba ta bukatar ta ga sakamakon rahoto da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya za su gabatar domin bayanan sirri da suka tara sun yi nuni da cewa Assad ya yi amfani da makaman.

Ficewar kwararrun su 13 a cewar rahotanni, wata kofa ce dake nuna yiwuwar kai hari a kasar ta Syria da Amurka ke shirin jagoranta a kowane lokaci daga yanzu.

A jiya juma’a shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce lallai akwai shirin daukan matakin soji a kasar ta Syria duk da cewa wasu kasashen basu amince da yin haka ba.

“Ba za mu amince da kashe yara kanana da mata da wadanda basu ji ba basu gani bat a hanyar yin amfani da makamai masu guba.” Inji Obama.

Kalaman na sa na zuwa ne lokaci kadan bayan Sakataren harkokin wajensa, John Kerry, ya zargi Syria da kashe mutane 1,429 cikin su harda yara kanana 426.

Kerry ya ce ba za su amince da duniyar da ake kashe mata da yara da iskar gas ba, inda ya bayyana harin a matsayin barazana ga Amurka.

“Wannan hari babban kalubale ne ga duniya.” Obama ya kara da cewa.

To sai dai kasar Rasha wacce babbar kawace ga kasar ta Syria ana ta bangaren ta bukaci Amurka da ta gabatar da hujjojin da ta tattara dake nuna cewa Assad ya yi amfani da makaman.

Shugaba Vladmir Putin a jawabin da ya yi, ya ce rashin gabatar da hujjojin na nufin Amurkan ba ta da wata hujja game da ikrarin da ta ke yi.

“Game da ikrarin da Amurkan ke yi, ai sai su nuna wa kwararrun Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaron majalisar hujjojin da suka tattara, idan kuwa suka kasa, hakan na nufin babu hujja ko daya.” Inji Putin a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a yau Asabar.

Jim kadan bayan ficewar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya masu bincike daga kasar ta Syria ne, hukumomin kasar suka bayyana cewa a shirye Syria take ta kare kanta daga duk wani hari da yammacin duniya ke shirin kai mata inda suka kara da cewa suna tsammani hari daga Amurka a yanzu haka.

“Muna sa ran za a kawo mana hari a kowane lokaci daga yanzu, kuma a shirye muke mu rama duk wani hari da aka kawo mana.” Wani jami’in tsaron kasar ta Syria ya gaywa Kamfanin dillancin labaran AFP.

Putin ya kara da cewa wannan zargi da Amurkan ke yi, magana ce ta "banza".

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.