Isa ga babban shafi
Turkiyya

‘Yan bindiga sun sace wasu matukan jirgin Turkiya

Wasu ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matukan jirgin Tukiya guda biyu a yau Juma’a a kasar Lebenon. Ministan cikin gidan lebenon Marwan Charbel ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa an yi garkuwa da matukan ne akan hanyarsu zuwa tashar jirgin birnin Beirut da misalin karfe uku na dare, Kuma wata majiya tace ‘yan bindiga hudu ne suka yi garkuwa da mutanen.

Sojojin kasar Lebanon suna sintiri a kan hanyar zuwa tashar jirgin Beirut inda aka sace matukan jirgin Turkiya
Sojojin kasar Lebanon suna sintiri a kan hanyar zuwa tashar jirgin Beirut inda aka sace matukan jirgin Turkiya REUTERS/Hasan Shaaban
Talla

Gwamnatin Turkiya ta yi Allah waddai da lamarin kuma ta bukaci ‘Yan kasarta su fice daga Lebenon saboda rikicin Syria da ya shafi kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.