Ban ki-moon ya nuna damuwarsa da shigar Hizbullah rikicin Syria
Janar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-moon, ya nuna matukar damuwarsa kan shigar kungiyar Hizbulla cikin rikicin Syria.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A wata sanarwa da majalisar ta fitar sa’oi kadan bayan rokoki biyu da aka harba kan yankin kungiyar ta Hizbullah Ban ya yi kira ga daukacin kungiyoyi da kasashe da su kaucewa ruruta rikincin kasar ta Syria.
“Janar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya cike da damuwa game da yadda rikicin ke kara tsananta.” Kamar yadda sanarwar ta nuna.
Ana zargin kungiyar ta Hizbulla wacce ke da tushe daga kasar Lebanon da taimakawa bangaren Shugaba Bashr al - Assad wajen samun nasara a kokarin da bangarorin biyu ke yi na mallake garin Qusayr, wanda ke kusa da kan iyakar kasar ta Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu