Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

Syria: Kasashen Turai na taro akan janye takunkumin aika makamai

A yau Litinin ne Ministocin kasashen Turai za su tattauna batun janye takunkumin da suka kakabawa Syria domin taimakawa ‘Yan tawaye da makamai kamar yadda Faransa da Birtaniya suka bukata. Sai dai kuma akwai yawancin kasashen na Turai da ke adawa da kudirin, inda tuni Ministan harakokin wajen Syria ya bayar da tabbacin zai halarci taron kasashen Duniya na zaman lafiya da za’a gudanar da Geneva a watan gobe. 

Taron Ministocin harkokin wajen Nahiyar Turai
Taron Ministocin harkokin wajen Nahiyar Turai m.ruvr.ru
Talla

Taron na zuwa ne a dai dai lokacin da Faransa ke shirin daukar nauyin wani kwarya-kwaryar taro gabanin taron da kasashen duniya za su gudanar domin samar da mafita ga rikicin kasar Syria.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce, Faransa ba ta yadda kasashen duniya su ci gaba da zura ido ana kashe dimbin jama’a a kasar ta Syria, saboda haka ya kamata su samar da mafita ta siyasa a game da wannan rikici.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Mu’allem wanda ke gudanar da ziyara a kasar Iraqi ke cewa, taron da kasashen duniya ke shirin gudanarwa a birnin Geneva dangane da makomar kasar a cikin kwanaki masu zuwa, abu ne mai matukar muhimmanci, kuma Damascus na goyon bayansa.

Yanzu haka dai rikicin na Syria na gab da daukar wani sabon salo sakamakon hari da roka da wasu suka kai a kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon, yankin da kungiyar Hizbullah mai goyon bayan Bashar al- Assad ke da dimbin magoya baya.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah Hassan Nasrullah da ke gabatar da jawabi sa’o’i kadan kafin wannan hari, ya ce ko shakka babu Bashar al- Assad ne zai yi nasara a wannan yaki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.