Isa ga babban shafi
Mali

Mali ta samu tallafin biliyan 3.2 na Euro daga kasashen duniya

Kasashen Duniya sun yi alkawarin tallafawa kasar Mali da yawan kudi biliyan 3.2 na euro, a wani yunkurin ganin an sake gina kasar ta Mali. Taron wanda aka yi shi a birnin Brussels wanda kuma ya samu jagorancin Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Faransa a da ya yi niyyar tara kudi da yawansu ya kai biliyan 2.6 na kudin euro ne, domin sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Mali da harkokin siyasar ta.  

Shugaban kasar Mali, Diacounda Traore
Shugaban kasar Mali, Diacounda Traore REUTERS/Adama Diarra
Talla

Sai dai Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce masu ba da tallafi na kasa da kasa sun yi rawar gani domin kudin da aka samawa kasar ta Mali, ya haura yadda aka kimanta inda yawansu ya kai biliyan 3.2 na kudin euro.

A cewar Hollande wannan na nuna cewa za a iya samun hadin kai tsakanin kasashen Nahiyar Afrika da Turai domin cimma wata manufa da ta shafe kowa da kowa.

Shugaban kasar ta Mali Diacounda Traore ya nuna farin cikinsa game da wannan tallafi inda ya ce za a yi amfani da kudaden wajen ganin an sake gina kasar ta Mali ta fuskokin daban daban.

A dai watan Yulin mai zuwa ne aka kebe a matsayin lokacin da za a gudanar da sabon zabe a kasar ta Mali domin dawo da cikakkiyar turbar demokradiya a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.