Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Sojan Faransa sun soma janyewa daga birnin Toumbouctou

Sojojin kasar Faransa, sun soma janyewa daga birnin Toumbouctou zuwa Gao domin bai wa takwarorinsu na kasar Burkina Faso damar gudanar da ayyukan tsaro a birnin wanda aka kwato daga hannun ‘yan tawaye.

Sojan Faransa a birnin Tombouctou.
Sojan Faransa a birnin Tombouctou. Diarra / Reuters
Talla

Sojojin Faransa akalla 80 a cikin motocin yaki guda 20 ne suka tashi daga birnin na Toumbouctou a jiya asabar a kan hanyarsu ta zuwa birnin na Gao mai tazarar kilomita fiye da 400, yayin da sauran sojojin kasar za su ci gaba da janyewa sannu a kankali daga birnin.
Ficewar dakarun na Faransa daga Toumbouctou, na a matsayin cika alkawalin da shgaban kasar Francois Hollande ya yi na rage yawan sojojin kasar daga Mali ne domin bai wa takwarorinsu na nahiyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya fagen ci gaba da tabbatar da tsaro a kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.