Isa ga babban shafi
Labanon-Syriya

Wasu rokoki biyu sun fada a wata unguwa da ke kudancin birnin Beirut.

Wasu rokoki biyu da aka harba, sun fada a wata unguwa da ke kudancin birnin Beirut na kasar Labanan, yankin da ake kallo a matsayin babar cibiyar kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah wadda yanzu haka dakarunta ke Syria domin mara wa shugaba Bashar Assad a fadan da yake yi da ‘yan tawaye.

Wani dan sanda a kusa da inda rokoki suka fado a Beirut.
Wani dan sanda a kusa da inda rokoki suka fado a Beirut. REUTERS/Mohammed Azakir
Talla

Rahotanni sun ce tun da sanyin safiya ne wasu da ba a tabbatar da ko su waye ba ne suka harba wadannan rokoki inda suka fada a unguwar Al-Shayyah har ma suka raunata mutane 4.
Harin dai ya zo ne sa’o’I kadan bayan da shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Narsullah ya gabatar da wani jawabi, inda ya ke cewa ko shakka babu, shugaba Assad ne zai yi nasara a kan abokan hamayyarsa.
Ministan cikin gidan kasar ta Labanan Marwan Sharbel, ya bayyanan harin a matsayin wani zagon kasa domin haddasa fitina a kasar wadda da ma take fama da rikicin addini da kuma na mazhaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.