Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Kungiyoyin fararen hula 35 sun bukaci in tube sarki Sanusi - Ganduje

Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya samu wasiku dake neman ya tsige sarkin Kano Muhhamad Sanusi daga kungiyoyin fararen hula dabam dabam har 35 saboda abin da suka kira ‘’karan tsaye da yake wa mahukunta’’.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da sarki Muhammadu Sanusi II su na musabaha.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da sarki Muhammadu Sanusi II su na musabaha. vanguard
Talla

Mai magana da yawun gwamnan Abba Anwar ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya aike wa jaridar Premium Times, sai dai sanarwar ba ta kunshi sunayen wadannan kungiyoyi da suka bukaci a sauke sarki Sanusi na 2 ba.

Gwamna Ganduje dai ya rage karfin sarki Sanusi na 2 ta wajen kafa karin masasrautu hudu tare da nada sarakuna masu daraja ta daya don su jagoranci masarautun.

Kafin kafa wadannan masarautu, sarki Sanusi ne babban sarki daya tilo a jihar.

Wannan mataki na gwamna Ganduje ya gamu da caccaka daga sassa dabam dabam na jihar da ma kasar, musamman daga wadanda suke ganin hakan zai kawo rarrabuwar kawuna.

Sai dai Ganduje ya kare matakin nasa, inda yake cewa al’umma ce ta bukaci masarautu.

Amma masu sharhi na cewa matakan Ganduje tamkar kokari ne na musguna wa Sanusi sakamakon caccaka da ya ke wa gwamnatinsa, da kuma rashin goyon baya da ya nuna mai yayin da yake neman a sake zabensa a matsayin gwamnan jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.