Isa ga babban shafi
Afrika

'Yan Afrika ta kudu dauke da makamai na zanga-zangar kyamar baki

Akalla mutane 2 sun rasa rayukansu, yayinda jami’an tsaro suka kame wasu da dama bayan wata zanga-zangar kin jinin baki da al’ummar kasar Afrika ta kudu dauke da muggan makamai suka gudanar a yammacin jiya Lahadi, inda su ke neman lallai baki su gaggauta barin kasar.

Masu zanga-zangar kin jinin baki a Afrika ta kudu
Masu zanga-zangar kin jinin baki a Afrika ta kudu Daily Post
Talla

Wasu kafofin labarai a kasar sun bayyana yadda aka fuskanci arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an ‘yan sanda lokacin da suka rika kone shaguna da kadarorin baki a birnin Johammesburg na kasar.

A cewar David Tambe shugaban ‘yan sandan kasar ta Afrika ta kudu da ya ke tabbatar da lamarin, ya ce mutane biyu sun mutu sakamakon harbin bindiga da sukar wuka ko da dai bai bayar da tabbacin baki ne ko ‘yan kasar ne suka rasa rayukansu a hargitsin ba.

David Tambe ya ce masu zanga-zangar sun rika kone shaguna motoci da sauran kadarorin jama’a galibi ma na ‘yan kasar ta Afrika ta kudu.

Yanzu haka dai akwai ‘yan Afrika ta kudun kusan dari 5 da ke hannun jami’an tsaro bisa zarginsu da farmakar baki da ke zaune a kasar, bayan da matakin ya fara haddasawa kasar tsamin alaka da takwarorinta kasashen Afrika musamman Najeriya.

Kawo yanzu dai Najeriyar ta janye jakadanta daga Kasar yayinda ta shawarci al’ummarta kan illar ci gaba da zama a Afrika ta kudun bayan kisan wasunsu tare da kone dukiyoyinsu da aka yi a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.