Isa ga babban shafi
Najeriya

Mahara a Najeriya sun hallaka mutane 19 a wata majami'ar Benue

Wasu ‘yan bindiga a jihar Benue da ke Najeriya sun kai farmaki wata majami’ar St. Ignatius Quasi Parish da ke yankin Ayar-Mbalom a karamar hukumar Gwer ta gabas tare da hallaka akalla mutane 19.

Jihar Benue dai na fama da hare-hare wadanda suka faro daga rikicin makiyaya da manoma kafin daga bisani ya juye zuwa hare-haren sari-ka-noke.
Jihar Benue dai na fama da hare-hare wadanda suka faro daga rikicin makiyaya da manoma kafin daga bisani ya juye zuwa hare-haren sari-ka-noke. Daily Post
Talla

Cikin mutanen goma sha tara a cewar rahotanni biyu daga ciki limaman cocin ne sai kuma 17 mabiya, kuma lamarin ya faru ne a lokacin da suka kammala ibadarsu ta safiya su ke shirin komawa gida.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun kuma kone gidaje fiye da 100, baya ga jikkata iyalai da dama.

Harin na yau na zuwa ne kwanaki 4 bayan wani hari da ake kyautata zaton makiyaya ne suka kai da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 10 a karamar hukumar Guma.

Haka zalika bai wuce kwanaki hudun ba, da wasu tarin mutane sanye da kayan jami’an tsaro suka isa karamar hukumar Naka ta yamma tare da lalata tarin gidaje.

Jihar Benue dai na fama da hare-hare wadanda suka faro daga rikicin makiyaya da manoma kafin daga bisani ya juye zuwa hare-haren sari-ka-noke, wanda a lokuta da dama ke haddasa asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.