Turai ta yi barazanar hana Visa ga kasashen afrika da suka ki bata hadin kai ta magance matsalar yan ci rani.
Kungiyar tarayyar turai ta yi barazanar hana wasu kasashen Afrika Visa shiga nahiyar, matsawar suka ki bada hadin kai, wajen kwashe bakin haure yan kasashen su da suka shiga turai ta barauniyar hanya su mayar dasu kasashensu.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta tarayyar turai na bukatar ganin ta samu hadin kan kasashen na Afrika ne wajen kwashe bakin hauren yan kasashensu domin magance matsalar da ta dada yin muni a 2015 matsalar bakin hauren da ake ganin ita ce irin mafi muni da nahiyar Turai ta gani tun bayan yakin duniya na 2.
A lokacin da yake jawabi a Bruxell Komishinan dake kula da kaurar jama’a na tarayyar turai Dimitris Avramopoulos ya ce, ya yi matukar mamaki a cewa kasashen kasashe ne dake da kyaukyawar hulda da turai amma su ki bada hadin kai wajen sake mayar da yan kasashensu gida dake saune a turai ba tare da takardun izinin zama ba.
Ya kara da cewa daga yanzu kungiyar zata gindaya sharadin kin bada visa ga duk wata kasa abikiyar hulda da taki amincewa ta kwashe yan kasarta da suka shiga kasashen na turai ta barauniyar hanaya.
A karkashin dokokin duniya ko na turai dai, babu inda aka ce kasashen turai su baiwa da baki yan ci rani matsugunni a cikin kasashensu, amma dokokin sun bukaci su karbi yan gudun hijirar dake tserewa yaki a kasashen da suka baro
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu