Shugabannin Afirka na son lalubo hanyar tabbatar da tsaro
Shugabannin ƙasashen Afirka da ke halartar taron A.U a Addis Ababa sun gudanar da wata tattaunawa kan samar da zaman lafiya da tsaro a faɗin nahiyar.
Wallafawa ranar:
Shugabannin sun tattauna a kan rikice-rikice da suka ƙi ci suka ki cinyewa a wasu yankuna, da matsalar ƴan gudun hijira, da kuma matsalar sauyin yanayi.
A lokacin zaman an zanta kan rikicin Somalia da Libya, da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da yankin tafkin Chadi da wasu yankunan da dama.
A ranar lahadi ne ake za a bude babban taron, yayin da a ranar Litini shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabon tambarin yaƙi da rashawa na ƙungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu