Isa ga babban shafi
Nijar-Chadi

Chadi ta janye dakarunta da ke yaki da Boko Haram daga Diffa

Bayanai daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa kasar Chadi ta fara janye daruruwan dakarun ta da ke yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Diffa.

Tankokin yakin Chadi da ke fada da Boko Haram a Kamaru
Tankokin yakin Chadi da ke fada da Boko Haram a Kamaru AFP PHOTO / STEPHANE YAS
Talla

Masu sa-ido na kallon matakin a matsayin wanda ke da nasaba da sanya sunan kasar Chadi a cikin kasashen da aka hana basu bizar zuwa Amurka, lura da cewa tun daga lokacin da aka Amurka ta sanar da haka ne Chadi ta bayyana cewa matakin zai iya shafar ayyukan samar da tsaro da ta ke yi.

 

Janye dakarun zai yi matukar illa ga zaman lafiyar yankin, kamar dai yadda Dan Majalisarsu Lamido Moumouni Harouna ya ce sun fara kokawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.