Isa ga babban shafi
Birtaniya-Kenya

Kasashen waje sun soma aikewa da sako zuwa Uhuru Kenyatta

Birtaniya a jiya asabar ta aike da sakon taya murna ga Uhuru Kenyatta bayan nasarar da ya samu a zaben kasar.Birtaniya ta jaddada goyan bayan tareda ci gaba da huldar diflomasiya da Kenya kamar dai yadda Ministan harakokin wajen Birtaniya Borris Johnson ya sanar.

Zanga-zangar magoya bayan Raila Odinga  a kasar Kenya
Zanga-zangar magoya bayan Raila Odinga a kasar Kenya www.reuters.com
Talla

A daya wajen an share daren jiya yan Sanda na fuskantar boren masu zanga-zanga a wasu unguwanin  birnin Nairobie.

Tawo mu gama da ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100 a cewar yan adawa, yayinda bangaren hukuma suka bayyana mutuwar mutane kusan 20.

Tun bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben , Raila Odinga ya karaucewa manema labarai ba tareda ya yi jawabi a kai ba.

Wasu kungiyoyin kasar sun nuna matukar kaduwa ganin ta yada yan sanda ke amfani da karfi da ya wucce kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.